Sojojin Najeriya 19 suka bace sanadiyar harin boko haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8530-sojojin_najeriya_19_suka_bace_sanadiyar_harin_boko_haram
Dakarun tsaron Najeriya sun sanar da bacewar Sojoji 19 a wani harin ba zata da kungiyar boko haram suka kai musu.
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 23, 2016 04:15 UTC
  • Sojojin Najeriya 19 suka bace sanadiyar harin boko haram

Dakarun tsaron Najeriya sun sanar da bacewar Sojoji 19 a wani harin ba zata da kungiyar boko haram suka kai musu.

Kakakin rundunar sojan Kanal Sani Usman Kuka-Sheka ya shaida wa manaima lbarai cewa mayakan boko haram din sun yi wa Sojojin su kwantan bauna a yayin da suke kan hanyar komawa sansanin su ne, bayan sun je farautar mayakan 'yan Boko Haram a yankin Alagarno na Jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya

Kuka-Sheka ya ce sojojin sun kashe 'yan Boko Haram da dama, sun kuma kwato manyan makamai da kanana da kayan abinci, sannan kuma suka lalata maɓoyar 'yan Boko Haram din a yayin wannan farmaki, daga cikin irin makaman da aka kama har da wata babbar mota mai dauke da bindigar kakkabo jiragen sama.

Cikin Sojojin 19 da suka bace uku masu matsayin officer ne.,ko baya ga wadanda suka bacen a kwai sojoji 19 da suka jikkata a yayin wannan farmaki kuma uku daga cikin su masu mikamin officer ne.

Rikicin boko haram din da ya fara tun a shekarar 2009 ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 20 tare da raba kimanin million biyu da dubu 600 da mahalinsu a Najeriyan.