An karfafa matakan tsaron a babban birnin Murtaniya
(last modified Sun, 24 Jul 2016 11:22:02 GMT )
Jul 24, 2016 11:22 UTC
  • An karfafa matakan tsaron a babban birnin Murtaniya

A yayin Shirye-shriyen gudanar da taron kungiyar kasashen Larabawa karo na 27, an karfafa matakan tsaron a birnin Nuwakchot fadar milkin kasar Murtaniya

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya habarta cewa Magabatan kasar Murtaniya sun jibke jami'an tsaro da 'yan sanda da dama a ko wani lungu na birnin Nuwakchot musamman ma a kan manyan hanyoyin da tawagar kasashen Larabawan za su bi domin tabbatar da tsaro.

Ko baya ga hakan magabatan Murtaniyan sun tsagaita zirga-zirga a wasu anguwani na birnin, wanda hakan ya yi babban tasiri ga harakokin kasuwanci na birnin.

Bisa sanarwar kafafen yada labaran Murtaniya, kwanaki biyu kafin gudanar da taron, dukkanin manyan hanyoyin dake isa zuwa ga zauren taron sun koma guraren zirga-zirgen jami'an tsaro, inda aka haramtawa dukkanin fararen hula kai kawo a wadannan hanyoyi.

A bangare guda, Rahotanni daga kasar Masar sun ce shugaban Kasar Abdulfatah Alsese ya ce ba zai halarci taron ba, ana sa ran zai aike da Firaministan kasar ko kuma Ministan harakokin wajen kasar Samih shukri.