Libya:Ma'aikatar Harkokin Wajen Ta Aikewa Da Jakadan Kasar Faransa Sammaci.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8608-libya_ma'aikatar_harkokin_wajen_ta_aikewa_da_jakadan_kasar_faransa_sammaci.
An Kirayi Jakadan Faransa Zuwa Ma'aikatar Harkokin Wajen Libya, Kan Shigar Kasarsa harkokin cikin gidan Tripoli.
(last modified 2018-08-22T06:58:39+00:00 )
Jul 24, 2016 14:35 UTC
  • Libya:Ma'aikatar Harkokin Wajen Ta Aikewa Da Jakadan Kasar Faransa Sammaci.

An Kirayi Jakadan Faransa Zuwa Ma'aikatar Harkokin Wajen Libya, Kan Shigar Kasarsa harkokin cikin gidan Tripoli.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Libya ta gayyaci jakadan Faransa a cikin kasar, domin nuna masa rashin jin dadin tsoma bakin da kasarsa ta ke yi a harkokin cikin gidanta.

Wata majiyar diplomasiyya ta ce; Jakadan Faransan a Libya Antoine Sivan, yana rayuwa ne a kasar Tunisia saboda dalilan tsaro, amma zai je kasar ta a nan gaba, domin amsa sammacin da aka aike masa.

A makon da ya gabata ne dai Kasar Faransa ta sanar da mutuwar sojojinta uku da su ke aiki a kasar ta Libya.

Kamfanin Dillancin Labarun Associated Press ya nakalto cewa; gwamnatin faransa tana cewa  sojojin nata  dai suna aiki ne domin bada kariya ga gwamnatin rikon-kwarya.

Kwana daya bayan sanarwar ta Faransa, mutanen kasar Libya sun gudanar da zanga-zanga suna yin tir da faransan.