Kungiyar MEND A Najeriya Na Tattaunawa Da Gwamnati
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8632-kungiyar_mend_a_najeriya_na_tattaunawa_da_gwamnati
Babbar kungiya 'yan a ware mai dauke da makamai a yankin Niger Delta na Najeriya wato MEND ta ce, ta fara kwarya kwaryar tattaunawa da gwamnati don share fagen shiga babbar tattaunawa tsakanin ta da gwamnatin Najeriyar.
(last modified 2018-08-22T06:58:39+00:00 )
Jul 25, 2016 02:18 UTC
  • Kungiyar MEND A Najeriya Na Tattaunawa Da Gwamnati

Babbar kungiya 'yan a ware mai dauke da makamai a yankin Niger Delta na Najeriya wato MEND ta ce, ta fara kwarya kwaryar tattaunawa da gwamnati don share fagen shiga babbar tattaunawa tsakanin ta da gwamnatin Najeriyar.

Mai magana da yawun kungiyar Jomo Gbomo, ya fadi hakan cikin wata sanarwa da ta da aka aikewa manema labarai cewar, inda ya ce wannan kwarya kwaryar tattaunawar ita ce za ta share fagen shiga babbar tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriyar da kungiyar ta MEND, wanda ake sa ran za ta zama sila na kawo karshen takaddamar da ta ki- ci- ta- ki -cinyewa game da rikicin yankin na Niger Delta mai arzikin mai.

A ranar Alhamis ne, shugaba Muhammadu Buhari ya fada a Abuja, babban birnin kasar cewa, za'a gudanar da tattaunawar ce tsakanin gwamnati da shugabannin kungiyar, ta hanyar kamfanonin mai da hukumomin tsaro na kasar domin lalibo hanyoyin da za su tabbatar da kawo karshen rikicin.

A kwanakin baya ma dai ministan wasanni da matasa na kasar Barista Solomon Dalung ya ce ya zanta da tsagerun domin jin bukatunsu don samun zaman lafiya mai dorewa a yankin.