Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Zanta Da Shugaban Majalisar Dattijan Nigeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8665-ministan_harkokin_wajen_kasar_iran_ya_zanta_da_shugaban_majalisar_dattijan_nigeriya
A ci gaba da ziyarar aikin da yake gudanarwa a tarayyar Nigeriya ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya gana da shugaban Majalisar Dattijan Nigeriya tare da gabatar masa da goron gayyatar zuwa Iran baya da bukatar karfafa taimakekkeniya a tsakanin kasashen biyu.
(last modified 2018-08-22T06:58:39+00:00 )
Jul 25, 2016 13:56 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Zanta Da Shugaban Majalisar Dattijan Nigeriya

A ci gaba da ziyarar aikin da yake gudanarwa a tarayyar Nigeriya ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya gana da shugaban Majalisar Dattijan Nigeriya tare da gabatar masa da goron gayyatar zuwa Iran baya da bukatar karfafa taimakekkeniya a tsakanin kasashen biyu.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Jawad Zarif da ya fara gudanar da ziyarar aiki a wasu kasashen nahiyar Afrika inda ta fara da tarayyar Nigeriya a yau Litinin ya gana da shugaban Majalisar Dattijan Nigeriya Bukola Saraki a birnin Abuja tare da gabatar masa da goron gayyatar takwaransa na Iran Dr Ali Larijani na ziyartar kasar Iran.

Har ila yau Zarif ya tattauna bukatar karfafa alaka da taimakekkeniya tsakanin Majalisun Nigeriya da na Iran yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta gudanar da taimakekkeniya a fuskar ilimi da fasaha gami da noma da Nigeriya.

A nashi bangaren shugaban Majalisar Dattijan Bukola Saraki ya bayyana fatansa na ganin ya ziyarci kasar Iran tare da mika sakon gaisuwarsa ga Dr Ali Larijani.