An Nada Sabon Mataimakin Shugaban Kasa A Sudan Ta Kudu
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya nada Taban Deng Gai a matsayin sabon mataimakinsa, wanda ya maye gurbin Reick Machar.
Rahotanni daga birnin Juba sun ce Salva Kiir ya nada Deng Gai a matsayin mataimakinsa ne bayan da Reick Machar da sauran manyan 'yan adawa suka bukaci hakan.
Reikck Machar dai ya yanke shawar safka daga kan mukaminsa na mataimakin shugaban ne biyo bayan dauki ba dadin da aka yi a farkon watan Yunin da ya gabata, a tsakanin magoya bayansa da kuma dakarun Salva Kiir, bayan da magoya bayansa suka zargi gwamnati da yunkurin kashe shi ta hanyar shirya masa wata manakisa.
Taban Deng dai shi ne ya kasance babban mai wakiltar 'yan tawaye a zantawar da aka kawashe tsawon lokaci ana yi tsakaninsu da bangaren gwamnati a birnin Addis Ababa na Habasha, kafin cimma yarjejeniyar sulhu ta karshe a cikin wanann shekara.