Tashe-Tashen Hankula Sun Tarwatsa Wasu Kauyuka A Kasar Dimokaradiyyar Congo
Majiyar gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta tabbatar da labarin cewa: Tashe-tashen hankula sun tarwatsa al'ummar kauyuka shida da suke lardin Kivu ta Arewa a yankin Gabashin kasar.
Majiyar gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a jiya Litinin ta bayyana cewa: Al'ummun kauyuka shida da suke yankin Bwito a shiyar lardin Kivu ta arewa a gabashin kasar ne tashe-tashen hankula suka raba su da muhallinsu a cikin 'yan kwanakin nan.
Majiyar ta kara da cewa: Tashe-tashen hankulan sun kunno kai ne sakamakon rikicin da ya faru tsakanin 'yan tawayen kabilar Mai Mai na kasar da gungun 'yan tawayen kasar Ruwanda na kungiyar Democratic Forces for the Liberation of Rwanda {FDLR} da suke mamaye da wasu yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
A halin yanzu haka dai manyan kabilun yankin da mahukuntan kasar suna ci gaba da gudanar da zaman tattaunawa da nufin neman hanyar warware rikicin da ya kunni kan domin dawo da zaman lafiya da sulhu.