Taron Sulhu A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8749-taron_sulhu_a_kasar_mali
An sami Ci gaba a taron sulhu da aka yi akan kasar Mali
(last modified 2018-08-22T06:58:40+00:00 )
Jul 27, 2016 07:47 UTC
  • Taron Sulhu A Kasar Mali

An sami Ci gaba a taron sulhu da aka yi akan kasar Mali

Kamfanin Dillancin Labarun Xinuha na kasar Sin ya nakalto cewa; an kawo karshen taron sulhu da aka yi a tsakanin gwamnatin kasar Mali da kuma 'yan tawaye.

Taron na kwanaki biyu ya zo karshe tare da samun nasara da ci gaba akan abubuwan da aka tattauna da kuma aiwatarwa.

Daga cikin abubuwan da aka cimmawa a wurin taron, da akwai kafa rundunar sintiri ta baidaya tsakanin sojojin gwamnati da kuma 'yan tawaye da za ta kunshi mutane 600. Rundunar za ta fara aiki daga ranar 15 ga watan Augusta 2016 a yankin Gao da ke arewacin kasar.

Bugu da kari, taron ya bukaci a kafa gwamnatin rikon kwarya a yankin arewacin kasar a cikin gaggawa.

A tsakiyar watan Mayu na 2015 ne dai bangarorin gwamnati su ka cimma yarjejeniyar sulhu da tsagaita wutar yakin bayan shekaru uku na fada a tsakaninsu.