An zargi gwamnatin Sudan ta kudu da kashe fararen hula da dama.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i88-an_zargi_gwamnatin_sudan_ta_kudu_da_kashe_fararen_hula_da_dama.
Kwamitin da ke sanya idanu akan tsagaita wutar yaki a kasar Sudan ta kudu, ya zargi gwamnatin kasar da kashe fararen hula 50.
(last modified 2018-08-22T06:57:44+00:00 )
Feb 01, 2016 14:29 UTC
  • An zargi gwamnatin Sudan ta kudu da kashe fararen hula da dama.

Kwamitin da ke sanya idanu akan tsagaita wutar yaki a kasar Sudan ta kudu, ya zargi gwamnatin kasar da kashe fararen hula 50.

Jaridar Yau-Sabii ta kasar Masar ta buga wani rahoto na kwamitin da ya ke sanya idanu akan tsagaita wutar yakin Sudan ta kudu da ake kira, (JMEC) yana cewa; Sojojin gwamnatin kasar sun tsare mutane 50 a cikin yanayin zafi mai tsanani wanda ya yi sanadin mutuwarsu.

Rahoton ya kuma ci gaba da cewa; Sojojin gwamnatin kasar ta Sudan ta kudu sun kashe mutanan ne a ranar 26 ga watan Augusta na 2015 a jahar Unity.

Bugu da kari, rahoton ya kuma kunshi bayani akan yadda aka rika yi wa mata fyade da kuma kwace kayan taimako na majalisar dinkin duniya.

Kwamitin ya kuma mika rahoton nashi ne ga kungiyar tarayyar Afirka domin sanar da ita halin da ake ciki a kasar ta Sudan ta kudu.