Majalisar Dinkin Duniya Ta yi Kira Da a Kalubalanci Bokoharam.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8800-majalisar_dinkin_duniya_ta_yi_kira_da_a_kalubalanci_bokoharam.
Majalisar Dinkin Duniya Ta Kira yi kasashen gabar tekun Chadi da su kalubalanci kungiyar Bokoharam.
(last modified 2018-08-22T06:58:40+00:00 )
Jul 28, 2016 07:39 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta yi Kira Da a Kalubalanci Bokoharam.

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kira yi kasashen gabar tekun Chadi da su kalubalanci kungiyar Bokoharam.

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua ya ambato mataimakin babban sakataren majalisar dinkin duniyar a harkokin siyasa, Jeffrey Feltman yana cewa; rundunar hadin guiwa da ta kunshi kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Nijar da Benin, sun yi nasarar kwato wurare masu yawa daga hannun Bokoharam.

Feltman  wanda ya ke jawabi a gaban taron kwamitin  tsaro na majalisar dinkin duniya ya kara da cewa; Kasashen da su ke a gabar tafkin chadi  suna da bukatuwa da  karin taimakon kungiyoyin kasa da kasa, domin warware matsalar da mutanen yankin su ke ciki, haka nan kuma wajen fada da bokoharam.

Shi ma babban jami'i mai kula da harkokin agaji na majalisar dinkin duniyar, Stephen O'bryan ya ce; Da akwai mutane miliyan 9 da su ke da bukatuwa da taimakon gaggawa a cikin yankin.