Gabon : Kotun Tsarin Mulki Ta Yi Watsi da Korafin 'Yan Adawa
kotun tsarin mulki a Gabon ta yi watsi da korafin mayan 'yan adawa na kasar guda uku kan soke takara shugaban kasar Ali Bongo Ondimba a zaben shugaban kasar na ranar 27 ga watan gobe.
Mayan 'yan adawan na kasar uku da suka hada da tsohon shugaban kungiyar tarayya Afrika Jean Ping, da tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Guy Nzouba Ndama da kuma tsohon ministan kasar Pierre-Claver Maganga Moussavou na dai zargin shugaban kasar mai barin gado Ali Bongo da cewa ba dan asalin kasar ne ba, don haka takara sa ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
Saidai kotun tsarin mulkin kasar ta ce 'yan adawa sun kasa bada cikakar hujja hakan, don haka takara shugaba Ali Bongo na nan daram.
'Yan adawa dai sun ce Ali Bongo da aka zaba a shekara 2009 bayan rasuwar mahaifinsa, dan asalin kasar Najeriya ne wanda dan ruko ne ga tsohon shugaban kasar Omar Bongo wanda aka gyara masa takardun don zama dan kasar ta Gabon.
'Yan takara 14 ne dai ciki har da shugaban kasar mai barin gadi Ali Bongo Ondimba kotun tsarin mulkin kasar ta amunce da takara su a zaben shugaban kasar na ranar 27 ga watan Agusta mai shirin kamawa.