Sudan Ta Kudu Na Cikin Mummunan Hali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8839-sudan_ta_kudu_na_cikin_mummunan_hali
Babban sakatare na MDD Ban Ki Moon, ya bayyana matukar damuwa game da mummunan halin da Sudan ta Kudu ke ciki a halin yanzu, yana mai cewa abubuwan da suka auku a kasar a baya bayan nan, na nuna yadda aka yi hasarar muhimmiyar dama, ta wanzar da zaman lafiya a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:40+00:00 )
Jul 29, 2016 01:10 UTC
  • Sudan Ta Kudu Na Cikin Mummunan Hali

Babban sakatare na MDD Ban Ki Moon, ya bayyana matukar damuwa game da mummunan halin da Sudan ta Kudu ke ciki a halin yanzu, yana mai cewa abubuwan da suka auku a kasar a baya bayan nan, na nuna yadda aka yi hasarar muhimmiyar dama, ta wanzar da zaman lafiya a kasar.

Mr. Ban wanda ke wannan tsokaci, cikin jawabin sa na bude zaman mahawarar kwamitin tsaron MDD, ya ce ya kadu bisa jin irin tarin rahotanni dake nuni ga yadda ake keta hakkokin bil'adama, da aikata fyade ga fararen hula a kasar.

Ban Ki Moon ya ce akwai bukatar gaggauta daukar matakan shari'a ga masu aikata irin wadannan laifuka, a hannu guda kuma wajibi ne shugabannin kasar su rungumi matakai na wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

A farkon wannan wata ne dai fada ya sake barkewa tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna a birnin Juba fadar mulkin kasar ta Sudan ta Kudu, lamarin da kuma ya hadasa hasara rayukan mutane 272, ciki hadda fararen hula 33.