Dakatar da Aikewa da Kayan Agaji Zuwa Najeriya
Majalisar Dinkin Duniya Za ta dakatar da aikewa da kayan agaji zuwa kasar Najeriya.
Kamfanin Dillancin Labarun Associated Press ya ambato majiyar asusun kananan yara na majalisar dinkin duniya; "Unicef" yana sanar da dakatar da aikewa da kayan agajnin saboda harin da aka kai wa maaikatansu a arewa maso gabacin kasar.
Sanarwar ta Unicef ta ci gaba da cewa; baya ga kayan agajin da aka kai wa hari, an kuma jikkata ma'aikatansu.
Hukumar ta "Unicef' ta ci gaba da cewa ba za su koma aikewa da kayan agajin ba har sai idan sun yi nazarin harkokin tsaro a Najeriya din.
Akan hanyar Bama zuwa Maiduguri ne dai aka kai wa ayarin kayan agajin na kungiyar Unicef hari.
Daya daga cikin ma'aikatan hukumar ta Unicef da kuma wani ma'aikacin hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ne su ka jikkata.