An Bankado Wasu Sabbin Ayyukan Cin Zarafin Yara A Afirka Ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i886-an_bankado_wasu_sabbin_ayyukan_cin_zarafin_yara_a_afirka_ta_tsakiya
Sabbin zargin 4 sun shafi ma'aikatan wanzar da zaman lafiya daga kasar jamhuriyar demokradiya Congo.
(last modified 2018-08-22T06:57:49+00:00 )
Feb 17, 2016 02:15 UTC
  • Dakarun MDD a wani sintiri
    Dakarun MDD a wani sintiri

Sabbin zargin 4 sun shafi ma'aikatan wanzar da zaman lafiya daga kasar jamhuriyar demokradiya Congo.

MDD a ranar talatan nan ta fitar da sabbin zargin har guda 4 na cin zarafi da ma'aikatan wanzar da zaman lafiyar majalissar suka yi a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Sabbin zargin har 4 sun shafi ma'aikatan wanzar da zaman lafiya daga kasar jamhuriyar demokradiya ta Congo, inji Farhan Haqq mataimakin Kakakin majailissar a ganawar da yayi da manema labarai.

Wadanda lamarin ya rutsa da su dukkan su kananan yara ne kuma mazauna sansanin Ngakobo wadanda suka rasa gidajen su dake Ouaka kuma an tabbatar da cewar ma'aikatan sun ci zarafin su ne tsakanin shekara ta 2014 da 2015.

A cewar Mr Haq ofishin wanzar da zaman lafiyar na aiki tare da sauran hukumomin MDD da abokan huldar su domin tabbatar da cewar wadanda hakan ya faru akan su sun samu ingantacciyar kulawa kan lafiyar su da kuma tunanin su.