An Sake Kwato Wasu Garuruwa Dag Hannun Kungiyar Boko haram.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8887-an_sake_kwato_wasu_garuruwa_dag_hannun_kungiyar_boko_haram.
Sojojin Afirka Sun Kwato Wasu Garuruwa Daga Kungiyar Boko haram A Najeriya.
(last modified 2018-08-22T06:58:40+00:00 )
Jul 30, 2016 05:52 UTC
  • An Sake Kwato Wasu Garuruwa Dag Hannun Kungiyar Boko haram.

Sojojin Afirka Sun Kwato Wasu Garuruwa Daga Kungiyar Boko haram A Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin, ya ce; rundunar kasashe Afirka mai fada da boko haram da ta kunshi kasashen Najeirya da Chadi da Nijar da Kamaru da Benin, sun fitar da wani bayani a jiya juma'a a birnin Niyame, na kasar Nijar, da a ciki su ka tabbatar da kwato garuruwan Doutsi da Damasak daga hannun Boko haram.

Bayanin ya ci gaba da cewa; Sojojin Nijar, da sauran rundunar Afirkan ke agazawa, sun yi nasarar kwace garuruwan Duotsi da kuma Damasak.

Tun a ranar litinin din da ta gabata ne dai sojojin Nijar din da su ka yi amfani da tankokin yaki da motoci masu sulke, su ka fara kai farmaki akan 'yan kungiyar ta boko haram.