Harin Sojojin Gwamnatin Congo A Gundumar Kivo Ta Arewa
Jul 30, 2016 05:53 UTC
Majiyar Sojan Kasar Demokradiyyar Congo Ta Ce; An Kai Hari Akan Sansanonin 'Yan tawaye A Arewacin Kivo
Radiyon Okapi ya ambato majiyar sojan kasar Jamhuriyar demokradiyyar congo na sanar da cewa; Kungiyar 'yan tawyaen Mai-Mai, ta mamaye yankin Nyamilima da ke gundumar Kivo ta Arewa bayan janyewar sojojin kasar.
Sojojin sun ja daga ta tsawon sa'o'i biyu da 'yan tawayen a yankin na Nyamilima, wanda ya yi sanadin batan soja guda.
Majiyar sojan ta ci gaba da cewa; 'yan tawayen kungiyar ta Mai-mai, sun cinnawa yankin wuta.
Tuni dai mazauna yankin su ka koma gida, bayan korar 'yan tawayen.
Yankin gabacin kasar Demokradiyyar Congo ya zama wata tunga ta 'yan tawayen kasar da kuma na kasashen makwabta.
Tags