Shugaban Sudan Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Kalubalantar Duk Wani Mulkin Mallaka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8920-shugaban_sudan_ya_jaddada_aniyar_kasarsa_ta_kalubalantar_duk_wani_mulkin_mallaka
Shugaban Sudan Umar Hasan Albashir ya jaddada aniyar kasarsa ta ci gaba da kalubalantar mulkin mallakar kasashen yammacin Turai da Amurka.
(last modified 2018-08-22T06:58:41+00:00 )
Jul 31, 2016 00:40 UTC
  • Shugaban Sudan Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Kalubalantar Duk Wani Mulkin Mallaka

Shugaban Sudan Umar Hasan Albashir ya jaddada aniyar kasarsa ta ci gaba da kalubalantar mulkin mallakar kasashen yammacin Turai da Amurka.

A jawabin da ya gabatar a gaban taron jama'ar da suka tarbe shi a filin jirgin saman birnin Khartum fadar mulkin Sudan a jiya Lahadi: Shugaban kasar Umar Hasan Albashir ya yi furuci da cewa: Kasashen nahiyar Afrika zasu yantar da kansu daga duk wani kangin mulkin mallakar kasashen yammacin Turai da Amurka musamman a fuskar siyasa da tattalin arziki.

Bayan yin tofin Allah tsine kan hare-haren ta'addancin da ake ci gaba da kai wa kan kasashen Larabawa: Shugaban kasar ta Sudan ya jaddada wajabcin hadin kan kasashen Larabawa a fagen yaki da ta'addanci da nufin rusa 'yan ta'adda daga tushe.

Wannan furuci na shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya zo ne a daidai lokacin da ya hada kai da mahukuntan Saudiyya a fagen aiwatar da hare-haren wuce gona da iri kan Yamen da nufin samun damar shimfida mulkin kama karya kan kasar.