Sojojin Gwamnatin Somaliya Sun Kwato Wani Yanki Daga Mamayar 'Yan Al-Shabab
Sojojin gwamnatin Samaliya da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika sun kwato yankin Gresan-Wain da ke kudu maso yammacin kasar daga mamayar 'yan kungiyar ta'addanci ta Al-shabab.
Jami'in gudanarwa a gwamnatin Somaliya Abdi Muhammad ya sanar da cewa: Sojojin gwamnatin Somaliya da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika "AMISOM" a jiya Asabar sun samu nasarar kwato yankin Gresan-Wain da ke nisan kilomita 50 da yankin garin Hudhur a kudu maso yammacin kasar daga mamayar mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab.
A gefe guda kuma wakili na musamman na kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somaliya Francesco Madeira ya bayyana cewa: Tun daga lokacin tura dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na kungiyar tarayyar Afrika a shekara ta 2007 zuwa yanzu an samu nasarar wanzar da zaman lafiya da sulhu a yankuna da dama na kasar Somaliya sakamakon ayyukan hadin gwiwar da ke gudana tsakanin sojojin gwamnatin Somaliya da dakarun kungiyar tarayyar Afrika ta "AMINSOM".