Fiye Da Mutane Miliyan 50 Ne Ke Fuskantar Matsalar Abinci A Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8932-fiye_da_mutane_miliyan_50_ne_ke_fuskantar_matsalar_abinci_a_afirka
Hukumar Abinci Ta Duniya Ta yi gargadi Akan Karancin Abinci da Kasashe 17 na Afirka da larabawa za su fuskanta.
(last modified 2018-08-22T06:58:41+00:00 )
Jul 31, 2016 07:46 UTC
  • Fiye Da Mutane Miliyan 50 Ne Ke Fuskantar Matsalar Abinci A Afirka

Hukumar Abinci Ta Duniya Ta yi gargadi Akan Karancin Abinci da Kasashe 17 na Afirka da larabawa za su fuskanta.

Cibiyar Watsa labaru ta " al-Africa' ta ambato majiyar hukumar abincin ta duniya da ta fitar da wani bayani a ranar asabar tana cewa; Fiye da mutane miliyan 56 a cikin kasashen Afirka da na larabawa za su fuskanci karancin abinci.

Bayanin na hadin guiwa tsakanin kungiyoyin abinci na duniya "Wfp' da kuma "fao'  sun ambato sunayen larabawa da na Afirka. A cikin na larabawan da akwai Yamen da Syria da Iraki da Lebanon. Sai kuma kasashen Afirka da su ka hada Sudan da Sudan ta kudu da Mali da Brundi da Liberia. Haka nan kuma kasashen Afirka ta tsakiya da NIjar da Najeriya da Kamaru. Sai kuma kasashen Chad da Somaliya da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Bayanin ya kuma ce a kasar Yamen da kawai mutane miliyan 14 da su ke bukatuwa da taimakon gaggawa.