Ci gaban Da Libya Ta ke Samu A Fada Da Ta'addanci
Jul 31, 2016 12:18 UTC
Sojojin Gwamnatin Libya Sun Kai Sabbin Hare-hare Akan "Yan Da'esh A Garin Sirt.
Majiyar gwamnatin hadin kan kasa a Libya ta ce; Sojoji Suna Samun ci gaba a yakin da su ke yi da 'yan takfiriyyah da ke garin Sirt.
Sojojin sun yi amfani da jiragen yaki da kuma manyan bindigogi wajen kai wa 'yan 'takfiriyyah' din hari, abinda ya basu damar kara kutsawa cikin tsakiyar garin da kilo mita daya da rabi.
Tun a cikin watan Mayu ne dai, sojojin gwamnatin hadin kan kasa ta Libya din su ka fara samun galaba akan 'yan kungiyar ta "Da'esh' a cikin garin Sirt.
Tags