Somaliya : Mutane 13 Suka Mutu A Harin Bom A Mogadisho
Hukumomi a Somaliya sun tabbatar da mutuwar mutane 13 a jerin hare haren bom da aka kai a wata shedkwatar 'yan sanda a Mogadishu babban birnin kasar.
Rahotannin sun ce bakwai daga cikin mutanen da suka mutu wadanda suka kai harin ne.
An dai kai harin ne yau lahadi ne a harabar shedkwatar 'yan sanda masu kula da binciken miyagun laifuka a cewar rahotanni.
Ministan tsaro na kasar Abdirasak Omar Mohamed ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa harin ya rutsa da wasu fararen biyar da kuma dan Sanda guda.
har kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kai wannan harin, saidai sau tarin yawa akan nuna 'yar yatsa ga kungiyar nan ta Al'shabab mai alaka da babbar kungiyar 'yan ta'ada ta Al-Qaïda.
Wannan dai shi ne hari na biyu a wannan mako a cikin wannan kasa ta Somaliya bayan wani makamancinsa da yayi sanadin mutuwar mutane 13 a ranr talata data gabata.