Shugaban Kasar Gabon Ya Gargadi 'Yan Adawa Dangane Da Tayar Da Yamutsi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8971-shugaban_kasar_gabon_ya_gargadi_'yan_adawa_dangane_da_tayar_da_yamutsi
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Avndymba ya gargadi 'yan adawar kasar dangane da kalaman da ke fitowa daga bakunansu kan zaben shugaban kasa da za a gudanar a karshen wannan wata na Agusta.
(last modified 2018-08-22T06:58:41+00:00 )
Aug 01, 2016 01:23 UTC
  • Shugaban Kasar Gabon Ya Gargadi 'Yan Adawa Dangane Da Tayar Da Yamutsi

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Avndymba ya gargadi 'yan adawar kasar dangane da kalaman da ke fitowa daga bakunansu kan zaben shugaban kasa da za a gudanar a karshen wannan wata na Agusta.

Kamfanin dillanicn labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar ta Gabon ya bayyana zargin da wasu 'yan adawa ke yi kan cewa ba dan asalin kasar ba ne da cewa wannan magana ce maras tushe.

Ya kara da cewa wasu na hankoron ganin sun tunzura jama'a domin ganin ganin an samu cikas a zaben shugaban kasa mai zuwa, inda ya ce yin hakan ba maslaha ne ga kasar ba.

Hukumar zaben kasar Gabon dai ta tantnce mutane 14 daga cikin dukkanin mutanen da suka mika takardunsu na neman takarar shugabancin kasar,a  zaben da za a gudanar a ranar 27 ga wannan wata na Agusta.