NUC : Shaidar Karatun Digiri Ta Kwalejin Malamai Ta Kaduna Ba tada Inganci
Hukumar kula da jami'oi a nigeria ta bayyana cewa shaidar kammala karatun digiri na kwalejin malamai ta kaduna bata da inganci
Hukumar da ke kula da jami'oi na Nigeria NUC ta bayyana cewa shaidar samun digiri wacce colejin malamai da Kaduna take bayarwa ba tada inganci. Jairidar Daily Trust ta nakalto Ibrahim Yakasar jami'in hulda da jama'a na hukumar yana fadar cewa tun da dadewa hukumar ta sha shaidawa kolejin malamai ta Kaduna cewa bata da hurumin bada shaidan karatu na digirin farko ko fiye da shi don bata da jami'a wacce take damfare da ita kamar yadda yakamata ya kasance. Amma tayi kunnen uwan shegu da gargadin
Yakasai ya ce hukumarsa ta gudanar da zama ta musamman da shuwagabannin kolejin a shekara ta 2015, inda ta bayyana na masu hanyar da yakamata su bi don samun izinin bada shaidan digiri ga dalibanta. Jami'in ya kara da cewa duk wata makaranta wacce bada karkashin kula na wata jami'an tare da amincewar hukumar tasu to baya inganta da bada shaidan karatun digiri.
Daga karshe yakasai ya bayyana cewa wadanda suka karsbi shadar digiri ta kolegin malaman ta Kaduna basu cancanci shiga aikin bautar kasa ko aiki ko kuma ci gaba da karatu ba.