Rahoton Bincike Kan Abin Da Ya Faru A Rikicin Zaria
-
Abubuwan da suka auku a ranar 12 zuwa 14 ga watan Disambar bara tsakanin sojoji da \\\\\\\\\\\\\\\'yan Shi\\\\\\\\\\\\\\\'a a Zaria.
A wannan Litinin ce 2 ga watan Agusta 2016 gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta fitar da rahoton kwamitin nan da aka kafa domin gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru tsakanin sojoji da 'yan shia'a al'amajiran sheikh Ibrahim Zakzaky a Zaria a karshen shekara da bta gabata.
Rahoton wanda gwamnatin jihar ta karba a 'yan makwannin da suka gabata ya kunshi abubuwan da suka auku a ranar 12 zuwa 14 ga watan Disamban bara tsakanin sojojin Najeriya da 'yan kungiyar ta 'yan uwa musulmi a Zaria.
A cikin rahoto kwamitin ya zargi sojojin kasar da kisan 'yan shi'a 347 a rikicin da ya faru tsakanin sojojin da suka ce an tsare musu hanya kana an nemi hallaka babban hafsan sojin kasar janar Tukur Yusuf Buratai.
Hakazalika rahoton kwamitin binciken da gwamnatin Kaduna ta kafa ya ce an kashe soja guda a rikicin da aka shafe kwanaki biyu ana yi.
kwamitin ya kuma ce gwamnatin Kaduna ta bizne 'yan Shi'a 347 a wani kabarin gama gari, kana ya ce sojoji sun lalata wasu dukiyoyi na 'yan Shi'a da suka hada da rushe gidan shugabansu, Ibrahim Zakzaky, da cibiyar Husainiya, da kuma makarantar Fudiya.
Rahoto ya kuma ce sojojin sun yi amfani da karfi fiye da kima kan almajiran Ibarhim Alzazzaky.
Haka kuma kwamitin ya bukaci da a hukunta wadanda suka aikata wannan laifin, sannan a dauki mataki akan al'majiran Zazzaky saboda saba wa doka, kafin daga bisani rahoto ya soki shugaban kungiyar ta Harkar Musulunci ko kuma Islamic Movement a turance da kin tsawata ma almajiransa a lokacin rikicin.
A hannu daya kuma rahoton ya shawarci gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Kaduna a bisa yadda za a guji afkuwar irin wannan matsala a nan gaba.
Sai dai a nata bangaren Harkar Musulunci ta yi watsi da rahoton tana mai cewa mutanen da aka kashe mata sun tasamma dubu daya, yayin da ita kuwa rundunar sojin kasar ke musunta duk abin da ya faru.
Dama kafin hakan 'yan siyasa da masu fada aji da kungiyoyin kare hakkin bil adama na yankin da kuma kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International sun yi Allawadai da abin da sojoji suka yi wa al'amjiran na Sheikh Ibrahim Zakzaky a Zaria, tare yin kira da a kafa kwamitin musamman wanda baida bangaranci domin sanin hakikanin abin da ya faru.
Idan ana tune a watan Afrilu kungiyar Amnesty Int. ta fitar da wani rahoto wanda a ciki ta zargi sojojin Najeriya da kisan 'yan shi'a 350 da kuma bizne gawawakinsu a cikin makeken kabari, tare da lullube duk abin da ya faru.
Tun bayan afkuwar lamarin kusan watanni takwas har yanzu shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim Zakzaky na hannun jam'an tsaro duk da yanayin tabarbarewar lafiyarsa.
Kungiyar ta 'yan uwa musulmi ko Islamic Movement ta nuna damuwa a bisa lafiyar shugaban nata, wanda ta bukaci da a mika mata shi domin a nema masa lafiya a wajen kasar.
Baya ga shugaban kungiyar akwai wasu mabiyansa da ke tsare, haka nan kuma akwai matarsa ita ma da ke tsare, da harsashin bindiga a cikin jikinta, abin da ke bukatar a je waje da ita domin a yi mata aiki, sanan kuma akwai wasu mambobin kungiyar ta Islamic Movement da ta ce har yanzu ba tada labarinsu.