Sakamakon Binciken Kisan Zaria A Najeriya
Sakamon Binciken Kisan Zaria ya Bai wa Sojoji Laifi
Sakamakon binciken kisan Zaria, ya dora laifi akan sojojin Najeriya.
Telbijin din al'alam mai watsa shirye-shiryenta da turanci daga nan Tehran, ta bayyana cewa; Binciken ya bayyana cewa sojojin sun kashe 'yan shi'a 248 a cikin kwanaki uku a garin Zaria.
Gabanin wanann bnciken, kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Amnesty International' ta zargi sojojin Najeriya din da tafka laifi kan 'yan shi'a a cikin watan Decemba na 2015.
Bayanin kungiyar ta kare hakkin bil'adama ya ce; A ranakun 12 da 14 ga watan Decemna 2015, sojojin sun kashe 'yan shi'a 350 ba bisa ka'ida ba.
Daruruwan mutane ne dai aka kashe a lokacin harin da sojojin su ka kai a giran shugaban kungiyar 'yan'uwa musulmi Sheikh Ibrahim Yakub ak-zakzaky