Za a fara tattaunawa tsakanin 'yan adawa da Gwamnati a Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9061-za_a_fara_tattaunawa_tsakanin_'yan_adawa_da_gwamnati_a_sudan
Kungiyar Tarayyar Afirka ta sanya Rana na tattaunawa tsakanin bangaren Gwamnatin Sudan da 'yan adawa gami da 'yan tawayen kasar
(last modified 2019-03-18T02:12:56+00:00 )
Aug 03, 2016 00:55 UTC
  • Za a fara tattaunawa tsakanin 'yan adawa da Gwamnati a Sudan

Kungiyar Tarayyar Afirka ta sanya Rana na tattaunawa tsakanin bangaren Gwamnatin Sudan da 'yan adawa gami da 'yan tawayen kasar

Bayan tattaunawa da bangarorin 'yan tawaye gami da 'yan adawar Sudan, A jiya Talata Kungiyar tarayyar Afirka ta Ayyana ranar 8 ga watan Augusta a matsayin ranar da za a fara tattauna tsakanin Gwamnatin ta sudan da kuma bangaren 'yan adawa da na 'yan tawaye a birinin Adis Ababa na kasar Ethiopia.

A cewar Mahmoud Kan Shugaban Ofishin dake kula da hulda na kasashen Afirka a birnin Khartoum, wakilan kungiyar tarayyar Afirkan za su kasance a wannan zama kuma za su yi iya kokarinsu wajen ganin an cimma matsaya na tabbatar da sulhu a tsakanin bangarorin.

A makun da ya gabata Jam'iyun 'yan adawa da kuma kungiyoyin dake dauke da makamai na kasar Sudan din suka bayyana goyon bayansu da wannan zama bisa shiga tsakanin Kungiyar Tarayyar Afirka.

A watan Maris din da ya gabata Gwamnatin Kasar Sudan ta gabatar wa kungiyar Tarayyar Afirka shawarar zama kan tebirin shawara a tsakanin bangarorin kasar wanda hakan zai sanya a samu mafuta ga kasar domin tabbatar da konciyar hankali gami da zaman lafiya a tsakanin 'yan kasar Sudan din.