Ganawar Shugaba Buhari Da Jonathan A Yau A Abuja
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9094-ganawar_shugaba_buhari_da_jonathan_a_yau_a_abuja
Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta sirri da tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan a yau a fadar Aso Rock da ke Abuja.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Aug 03, 2016 12:04 UTC
  • Ganawar Shugaba Buhari Da Jonathan A Yau A Abuja

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta sirri da tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan a yau a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Shafin jaridar This Day da ake bugawa  a tarayyar Najeriya ya bayar da rahoton cewa, ganawar ta gudana ne a asirce a tsakanin shugaba Buhari da Jonathan a yau da rana, kuma babu wani karin bayani daga bangaren gwamnati dangane da dalilan ganawar.

Sai dai a lokacin da yake amsa tambayoyin wasu manema labarai Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa a ganawar tasu, ya yi wa shugaba Buhari bayani ne dangane da tafiye-tafiyen da ya yi ne a kasashen ketare a matsayinsa na manzon musamman na kungiyar tarayyar Afirka.

Yayin da kuma wasu suke hasashen cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da batun tsaro a yankin Niger-Delta ba, musamman ma ganin yadda Jonathan ya taka ma 'yan bindiga birki kan yunkurinsu na kafa kasar Niger Delta mai cin gishin kanta a ranar 1 ga wannan wata na Agusta, inda Jonathan ya hana su yin hakan.