An Nada Sabon Shugaban Boko Haram
Kungiyar 'yan ta'addan ISIS ta sanar nada sabon shugaban kungiyar Boko Haram da ke a matsayin reshen kungiyar a yammacin nahiyar Afirka.
Bayanin da kungiyar ta ISIS ta fitar a yau ya sanar da Abu Mus'ab Al-barnawi a matsayin sabon jagoran kungiyar a yammacin nahiyar Afirka a matsayin wanda ya maye gurbin Abubakar Shekau.
Kafin wannan lokacin dai Al-barnawi ya rika fitowa amtsayin mai magana da yawun kungiyar, tun bayan da Abubakar Shekau ya yi batan dabo, inda kuma daga bisani ya bayyana a cikin wani faifan bidiyoa yana a cikin halin na rauni matuka, inda daga nan kuma har yanzu ba a kari jin duriyarsa ba.
Kungiyar Boko Haram wadda ta sanar da yin mubaya'a ga kungiyar 'yan ta'addan takfiriyyah wahabiyya ta ISIS, ta kaddamar da hare-hare da dama a kan masallatai, kasuwanni da wuraren hada-hadar jama'a da kuma kone kauyuka, musamman a cikin yankunan arewa maso gabashin najeriya, da kuma wasu yankuna a cikin kasashen Kamaru, Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, akasarinsu fararen hula, yayin da miliyoyi kuma suka shiga gudun hijira.