Abubakar Shekau Ya Karyata Tsige Shi
Sananen jagoran kungiyar 'yan ta'addan nan da aka fi sani da boko haram wato Abubakar shekau, wanda (IS) ta sanar da maye gurbinsa ya karyata cewa an tsige shi.
Shekau dai ya musunta tsige shi ne a cikin wani sakon sauti na mintina goma a harshen hausa da larabci, inda ya zargi Abou Moussab al-Barnawi da almajiransa da shirya masa makarkashiya ta hanyar turawa kungiyar 'yan ta'adda ta IS bayanai na karya marasa tushe a kansa.
Wadannan kallamen na Shakau na zuwa kwana guda bayan da kungiyar IS ta sanar da Abu Musab al-Barnawi a matsayin sabon shugaban reshenta a yammacin Afrika.
A cikin sabon faifan bidiyon dai, Shekau wanda aka shafe shekara guda ba a ji duriyar sa ba ya kimanta Al'barnawi da cewa mushiriki ne.
Shekau ya kara da cewa lalle an bukace shi da ya tura akidarsa a rubuce ga jagoran na IS, aman ya ce wasu munafikansa suka bata akidar daya rubuta don cimma manufofinsu.
Sabon shugaban kungiyar dai Al'barnawi ya zargi shekau da sabawa manufofin kungiyar, kana ya kori wasu mashawartan dakaru na IS tare da kame masu abinci da kayan yaki, batutuwan da Shekau din ya musunta.