RDC : Kura Ta Lafa Bayan Barkewar Tashin Hankali A Kinshasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9130-rdc_kura_ta_lafa_bayan_barkewar_tashin_hankali_a_kinshasa
Rahotanni daga kinshasa a jamhuriya demokuradiyyar Congo na cewa an fara samun kwanciyar hankali, bayan barkewar tashin hankali da yammacin ranar Talata tsakanin magoya bayan jam'iyyar adawa da 'yan sanda.
(last modified 2018-08-22T06:58:42+00:00 )
Aug 04, 2016 01:21 UTC
  • RDC : Kura Ta Lafa Bayan Barkewar Tashin Hankali A Kinshasa

Rahotanni daga kinshasa a jamhuriya demokuradiyyar Congo na cewa an fara samun kwanciyar hankali, bayan barkewar tashin hankali da yammacin ranar Talata tsakanin magoya bayan jam'iyyar adawa da 'yan sanda.

Shedun gani da ido sun fadawa kamfanin dillancin labarun Xinhua cewar, jami'an 'yan sandan kasar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa magoya bayan jam'iyyar adawar ta Union for Democracy and Social Progress wato (UDPS) a takaice.

Sai dai ana samun bayanan dake cin karo da juna, game da musabbabin tashin rikicin, yayin da wasu rahotanni ke cewa mutun guda ya rasa ransa a tashin hankali.

baynai daga 'yan adawa na kasar sun tabbatar da hakan tare da cewa mutimun mai suna Guy Mpiana ya mutu ne sakamakon harbin bindiga da wani jami'in tsaro ya yi masa.