An Dage Shari'ar Masu Fafatukar Yaki Da Bauta A Mauritania
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9136-an_dage_shari'ar_masu_fafatukar_yaki_da_bauta_a_mauritania
A Mauritania an dage shari'ar wasu masu fafatukar yaki da bauta a kasar har zuwa ranar takwas ga watan Agustan nan da muke ciki.
(last modified 2018-08-22T06:58:42+00:00 )
Aug 04, 2016 01:22 UTC
  • jagoran kungiyar yaki da bauta ta IRA a moritaniya
    jagoran kungiyar yaki da bauta ta IRA a moritaniya

A Mauritania an dage shari'ar wasu masu fafatukar yaki da bauta a kasar har zuwa ranar takwas ga watan Agustan nan da muke ciki.

Mutanen dai 13 na wata kungiyar IRA ta yaki da bauta a kasar, ana dai zargin su ne da tada zaune tsaye da kuma farmawa cibiyoyin gwamnati .

An dai soma shari'ar ne a jiya Laraba cikin kwararen matakai na tsaro, inda dubban jama'a 'yan uwa da obokan wadandan ake tuhuma suka halarci wurin shari'a inda aka zuba jami'an tsaro na 'yan sanda masu yawa.

A wata sanarwa da suka fitar kungiyoyi da dama a ciki da wajen kasar ciki har da Amnesty International sunyi allawadai da tsarewar da akewa mutanen tare da neman a sake su ba tare da wata wata ba.

An dai cafke mutanen ne tsakanin karshen watan Yuni zuwa Yuli bisa shiga wata mumunnar zanga zanga a lokacin da ake kwashe mutanen wata unguwar marasa galiho a Nouakchott inda 'yan sanda da dama suka raunana.