Rikicin Siyasa Na Kara Munana A Kasar Zimbabwe
Rahotanni daga kasar Zimbabwe na nuni da cewa rikicin siyasa na kara muni a kasar biyo bayan taho mu gamar da ke ci gaba da faruwa tsakanin masu zanga-zangar kin gwamnatin kasar da jami'an tsaro a birnin Harare, babban birnin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar rikicin dai ya barke ne lokacin da jami'an 'yan sandan suka fada wa masu zanga-zangar wadanda suke dauke da kwalayen da suke dauke da nuna rashin amincewarsu da mummunan yanayin rayuwa da suke ciki da kuma kiran shugaban kasar Robert Mugabe da yayi murabus.
Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da zanga-zangar da suke yi har sai sun cimma burinsu na ganin gwamnatin ta kyautata rayuwar al'umma da kuma ganin shugaba Mugaben wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana mulkin kasar ya sauka daga karagar mulki.
A nata bangaren gwamnatin Zimbabwen ta bayyana wannan zanga-zangar a matsayin wani kokari na 'yan adawa ne na mai da hannun agogo baya a kasar.