Aug 04, 2016 15:28 UTC

Shekau dai ya musunta tsige shi ne a cikin wani sakon sauti na mintina goma a harshen hausa da larabci, inda ya zargi Abou Moussab al-Barnawi da almajiransa da shirya masa makarkashiya.

Wadannan kalaman na Shekau na zuwa kwana guda bayan da kungiyar IS ta sanar da Abu Musab al-Barnawi a matsayin sabon shugaban reshenta a yammacin Afrika.

A cikin sabon sautin dai, Shekau wanda aka shafe shekara guda ba a ji duriyar sa ba ya kimanta Al'barnawi da cewa mushiriki ne.

Tags