Damuwar Unucef kan ciyar ga mumunan abinci ga kananen yara A Afirka
Kungiyar Unucef Ta Bayyana Damuwarta game da ciyar da kananen yara Abinci maras gina jiki a kasashen Afirka
A wata sanarwa da ya fitar yau Laraba Asusun kananen yara na Majalisar Dinkin Duniya wato Unusef ya bayyana cewa kimanin kananen yara million guda ke fuskantar matsalar abinci mai gina jiki a yankunan gabas da kudancin Afirka.
Leila Gharagozloo-Pakkala babbar Daraktar Unusef a yankin Afirka ta bayyana cewa tsancin yanayi da matsalar fari sune babbar matsalar da suka sanya kananen yaran suka shiga cikin wannan mawuyacin hali.
Kungiyar Unusef ta ce wannan yanayi na canjin yanayi zai ci gaba har cikin watan Maris mai kamawa.
Kasashen Malawi, Madagascar da kuma Zimbabwe sune kasashen da suka fi fuskantar matsalar sauyin yanayi da fari a kasashen na Afirka.