Ambaliyar Ruwan Sama Ta Ci Rayuka A Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9172-ambaliyar_ruwan_sama_ta_ci_rayuka_a_sudan
Ambaliyar Ruwan Sama Ta Ci Rayuka A cikin Gundumomi 13 A Kasar Sudan
(last modified 2018-08-22T06:58:43+00:00 )
Aug 04, 2016 13:43 UTC
  • Ambaliyar Ruwan Sama Ta Ci Rayuka A Sudan

Ambaliyar Ruwan Sama Ta Ci Rayuka A cikin Gundumomi 13 A Kasar Sudan

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin, daga kasar Sudan, ya nakalto ministan Harkokin cikin gida Ismat Abdurrahman, yana  sanar da mutuwar 'yan kasar 76 sanadiyyar ambaliyar ruwan sama, tare kuma da rushewar gidaje 1300.

Ita ma hukumar bada agajin kasar ta Sudan, ta yi gargadi akan mummunan halin da mutane su ka shiga  a yankunan da ambaliyar  ta faru, tare da jaddada wajabcin ci gaba da ayyukan agaji.

Tuni dai majalisar dinkin duniya ta fitar da wani rahoto da a ciki ta bayyana cewa; yanayin el-nino da ke faruwa a cikin dabi'a na sauyin yanayi, zai sa a sami karin mutane miliyan 60 da za su fuskanci matsalar yunwa a duniya.