Sama Da Mutane 300 Aka Ceto Daga Hanun Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i922-sama_da_mutane_300_aka_ceto_daga_hanun_boko_haram
Dakarun tsaron Najeria Sun Samu Nasarar Mutane 350 A Wani Sumame Da suka kaiwa mayakan kungiyar boko haram.
(last modified 2018-08-22T06:57:49+00:00 )
Feb 17, 2016 14:07 UTC
  • Sama Da Mutane 300 Aka Ceto Daga Hanun Boko Haram

Dakarun tsaron Najeria Sun Samu Nasarar Mutane 350 A Wani Sumame Da suka kaiwa mayakan kungiyar boko haram.

A wata Sanarwa da ya fitar yau, kakakin Rundunar Sojin Najeria, Kanal Kukasheka Usman ya bayyana cewa fiye da fararen hula 350 ne suka ceto daga hanun maykan kungiyar boko haram a ci gaba da kokarin da sojoji ke yi na tsarkake yankunan kasar daga hanun mayakan kungiyar boko haram, daga cikin wadanda aka ceton har wasu kananen 'yan Mata 5 da kungiyar boko haram din ta sace daga kasar Kamaru.

Kanal Kukasheka Usman ya kara da cewa sun hallaka mayakan boko haram biyar bayan da suka cabke wasu biyu na daban.

Rahoton ya ce kimanin kauyuka 15 ne dake jihar Borno aka tsarkake daga mayakan kungiyar boko haram bayan da aka rusa sansanoninsu masu yawa a arewa maso gabashin kasar.

Wannan farmaki da Sojin Najeria suka kaiwa kungiyar Boko haram din na zuwa ne bayan wani irinsa da takwarorinsu na kasar kamaru suka kai a arewa mai nisa inda suka ceto fararen hula 112 daga hanun mayakan boko haram din tare da rusa sansanonisu da kuma kame motoci , babura da makamai masu yawa.