Fatan Kasashen Afirka Na Kawo Karshen Rikicin Cikin Gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9232-fatan_kasashen_afirka_na_kawo_karshen_rikicin_cikin_gida
Jami'an Tsaro Na Kasashen Afirka 51 Sun yi Taro A Birnin Kigali Na Rwanda.
(last modified 2018-08-22T06:58:43+00:00 )
Aug 06, 2016 01:04 UTC
  • Fatan Kasashen Afirka Na Kawo Karshen  Rikicin Cikin Gida

Jami'an Tsaro Na Kasashen Afirka 51 Sun yi Taro A Birnin Kigali Na Rwanda.

Jami'an Hukumomin Tsaro na kasashen Afirka 51 Sun bukacin ganin an dauki kwararan matakai domin kawo karshen rikicin cikin gida a wasu kasashe. Taron  dai an bude shi ne a cikin birnin Kigali na Kasar Rwanda a ranar litinin 1 ga watan Augusta kuma za a kawo karshensa a yau asabar.

Juan Antonio Bibang Nchuchuma wanda shi ne shugaban kwamitin, ya bayyana cewa  da ke tattauna rikice-rikice da kuma aikata laifuka su na haddasa rashin tabbas na siyasa a cikin nahiyar ta Afirka,  saboda haka wajibi ne a samo hanyar warware wadannan matsaloli.

A halin da ake ciki a yanzu, kasashe irin su  Jamhuriyar Demokradiyyyar Congo da Brundi da Afirka ta tsakiya da Sudan ta kudu, suna cikin yanayin da ya dara na sauran kasashen tabarbarewa. kwararru kuwa suna bada shawarar cewa matukar ba a dauko wadannan matsalolin daga tushensu ba, tokawo karshen rikice-rikice a nahiyar ba abu ne mai yiyuwa ba.

Tashe-tashen hankula dai a nahiyar Afirka suna da bangarori da dama:

Na farko; "Yan mulkin mallaka suna da hannu wajen haddasa rashin tabbas na siyasa da rikicin iyakoki da talauci da kuma koma baya na tattalin arziki. Wasu abubuwan da su ke haddasa irin wadannan rikice-rikicen sun hada da rashin aikin cibiyoyi da kungiyoyin yanki da kuma na kasa da kasa kamar yadda ya kamata wajen daidaita banbance-banbance na kabilu da al'adu da ake da su.

Mafi yawancin kasashe masu tasowa suna da banbance-banbance na kabilu da al'adu, amma hakan ya fi yawa a cikin nahiyar Afirka. Wannan ne ya sa a wanann zamanin aka fi samun rikice-rikicen kabilanci mafi hatsari a cikin nahiyar ta Afirka. Kabilanci, shi ne tushen mafi yawancin rikice-rikice a cikin nahiyar, domin kuwa suna shafar bangarori daban-daban na rayuwar al'umma.

Wasu dalilan na bayyanar rikcice-rikice a cikin nahiyar sun hada da yaduwar makamai a hannun fararen hula. Haka nan rashin aikin tsarin demokradiyya kamar yadda ya dace a cikin nahiyar yana taka rawa a wannan fage. Rashin kishin kasa da yaduwar cutuka da rashin aikin yi da sabanin kan iyakoki a tsakanin kasashe wasu bangarori ne na wannan rikicin.

A dalilin haka, da akwai bukatar yin tunani mai zurfi domin warware wadannan matsalolin daga tushensu.