Habasha : An Cafke Masu Zanga-zanga Da Dama
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9247-habasha_an_cafke_masu_zanga_zanga_da_dama
Rahotannin daga Habasha na cewa 'yan sanda sun cafke mutane da dama da kuma lakadawa wasu duka a lokacin da suka fito zanga-zanga yau Asabar a babban dandalin birnin Addis Ababa domin nuna kin jinin gwamnati.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 06, 2016 11:21 UTC
  • Habasha : An Cafke Masu Zanga-zanga Da Dama

Rahotannin daga Habasha na cewa 'yan sanda sun cafke mutane da dama da kuma lakadawa wasu duka a lokacin da suka fito zanga-zanga yau Asabar a babban dandalin birnin Addis Ababa domin nuna kin jinin gwamnati.

Wannan dai ita ce zanga-zanga irin ta, ta farko tun dai bayan da mayan kabilu na kasar Oromia da Amhara dake zamen kashi 80% na al'ummar kasar suka fara kiran gwamnati, akan a kawo karshen abinda suka kira kisan al'ummarsu da kuma mutunta 'yancin biladama.

Tun a ranar Juma'a ne firaministan kasar Haile Mariam Dessalegn ya sanar da haramta zanga-zanga tare da baiwa 'yan sanda kasar umurnin amfani da duk hanyoyin da suka dace domin hana zanga zanga.

Ko baya ga hakan hukumomin kasar sun toshe kafofin sada zumunta sakamakon zanga-zangar.

Wasu rahotanni na daban sun ce an gudanar da irin wannan zanga-zanga a birane da dama na kasar.