Gyaran Fuska A Cikin Rundunar Sojin Kasar Ivory Coast
Ma'aikatar tsaro a kasar ivory Coast ta sanar da cewa ta fara gudanar da wani shiri na yin gyaran fuska a cikin ayyukan rundunar sojin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoto daga birnin Abijan babbar cibiyar kasuwanci ta kasar Ivory Coast cewa, a jiy ma'aikatar harkokin tsaron kasar ta Ivory Coast ta sannar da hakan, inda ta ce gyare-gyaren da za a yi za su taimaka wajen mayar da rundunar sojin kasar ta zama daidai da sojoji na duniya.
Hakan kuwa ya hada horo, samar da kayan aiki na zamani, da kuma gina sabbin barikoki wadanda za su yi daidai da barikokin soji na kasashen da suka ci gaba da fuskar soji, wanda hakan zai kyautata ayyukan sojojin kasar a ciki da wajen kasar.