Hukumar Zabe A Somaliya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa
Aug 08, 2016 09:36 UTC
Hukumar zaben kasar Somaliya ta sanar da karshen watan Oktoban wannan shekara a matsayin lokacin gudanar da zaben shugabancin kasar.
Hukumar zaben kasar Somaliya a ta bakin shugaban hukumar ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaben shugabancin kasa a karshen watan Oktoban wannan shekara ta 2016 da muke ciki wanda zai kama ranar 30 ga watan.
Har ila yau shugaban Hukumar zaben kasar ta Somaliya Umar Muhammad Abdullahi ya fayyace cewa: Za a gudanar da zabukan 'yan Majalisun Dokokin kasar ne a ranar 25 ga watan Satumban wannan shekara.
Tags