DRC : An Soke Izinin Wata Mai Bincike Ta HRW
Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ta hana wata mai bincike kan keta hakkin bil Adama ci gaba da gudanar da aikinta a kasar.
Tuni dai kungiyar ta Human Right Watch tayiAllawadai da wannan matakin.
A jiya Talata ne kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Right Watch, ta ce gwamnatin jamhuriyar dimokaradiyar Congo ta soke izinin da aka baiwa Ida Sawyer, wace ta dade tana yin aikin ta a kasar tun shekara 2008.
Kungiyar ta Human Right Watch ta ce haka kurum jami’an kula da shige da ficen baki suka ce an dakatar da sabon izinin bincikenta, a lokacin da zata yi tafiya daga babban filin saukar jiragen sama na Kinshasa.
Kungiyar ta ce Sawyer ta cike takardun sake samun izinin bincike a kasar, amma aka hanata ranar Litinin din da ta gabata, aka kuma bukaci ta bar kasar cikin kwanaki biyu.
babu dai wani karin bayyani daga hukumomin kasar dangane da wannan matakin.