Sudan Ta Kudu: Sabon Fada Ya Barke A Kudu Maso Yamma
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9397-sudan_ta_kudu_sabon_fada_ya_barke_a_kudu_maso_yamma
Rahotanni daga Sudan ta kudu na cewa wani sabon fada ya barke tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen a kudu maso yammcin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 10, 2016 01:14 UTC
  • Sudan Ta Kudu: Sabon Fada Ya Barke A Kudu Maso Yamma

Rahotanni daga Sudan ta kudu na cewa wani sabon fada ya barke tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen a kudu maso yammcin kasar.

An dai gwabza fadan ne tsakanin dakarun shugaban Salva Kiir da kuma na tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar a wurare biyu dake kusa da juna a birnin Yei dake nisan kilomita 150 daga kudu maso yammacin Juba babban birnin kasar.

Abin tuni, wani fada daya barke a tsakanin ranakun 8 zuwa 11 ga watan Yuli, yayi sanadin mutuwar mutane 300 tare da cilastawa wasu fiye da 60,000 tserewa daga muhallansu.

 Tun dai lokacin ne jagoran 'yan tawayen, kana tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar ya fice daga birnin Juba, kuma bayan hakan ne shugaba Salva Kiir ya nada ministan ma'adunai na kasar a matsayin sabon mataimakinsa

Wannan lamari dai ya haifar da koma baya ga yunkurin samar da zamen lafiya da aka dade ana bukata a wannan jinjirar kasa, tun bayan yakin basasar daya barke a watan Disamba na 2013.