Kasashe 25 Na Afrika Na Tattaunawa Kan Yaki Da 'Yan Fashin Teku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9403-kasashe_25_na_afrika_na_tattaunawa_kan_yaki_da_'yan_fashin_teku
Kwararru da masana daga kasashe 25 na kungiyar kula da yankunan teku na Afrika ta yamma da ta tsakiya (OMAC), na halartar wani taro a Lome babban birnin kasar Togo domin dakile yawaitar yin fashi a teku.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 10, 2016 01:22 UTC
  • Kasashe 25 Na Afrika Na Tattaunawa Kan Yaki Da 'Yan Fashin Teku

Kwararru da masana daga kasashe 25 na kungiyar kula da yankunan teku na Afrika ta yamma da ta tsakiya (OMAC), na halartar wani taro a Lome babban birnin kasar Togo domin dakile yawaitar yin fashi a teku.

Taro na kwanaki hudu da aka fara jiya Talata, ya kasance tamkar share fage ne ga taron da kungiyar tarayyar Afrika AU za ta gudanar game da yaki da 'yan fashin teku da kuma ci gaban Afrika, wanda za a gudanar a Lome a cikin watan Octoba mai zuwa, da nufin kawo karshen yin fashi a yankunan teku.

Masanan za su tattauna ne game da hanyoyin magance yawaitar matsalolin 'yan fashin teku, wanda yake daya daga cikin illolin dake addabar kasashe masu tasowa.

Minista mai kula da zirga-zirga na kasar Togo ya ce, yaki da 'yan fashin teku, wani babban kalubale ne wanda ya kamata a yi taka tsan-tsan duk da fuskantar karancin kayayyakin aiki.