Karuwan Zanga-zangar al'ummar Kasar Habasha
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9421-karuwan_zanga_zangar_al'ummar_kasar_habasha
AL'ummar Oromo a rewacin Habasha
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 10, 2016 14:36 UTC
  • Karuwan Zanga-zangar al'ummar Kasar Habasha

AL'ummar Oromo a rewacin Habasha

Al'ummar Oromo da ke arewacin kasar Habasha na ci gaba da yin zanga-zangar nuna kin jinin hukuma.

Kafar watsa labaru ta "N.P.R. ta ambato cewa; Zanga-zangar ta mutanen Oromo tana ci gaba ne adaidai lokacin da ake kara samun  koma bayan sabanin kabilanci a cikin kasar.

"Yan sandan kasar na shirin amfani da karfi domin murkushe masu zanga-zangar.

A cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata ne dai al'ummar Oromo su ka fara zanga-zanga domin nuna kin amincewa da shirin fadada babban birnin kasar Adiss Ababa.

Orormo da ita ce kabila mafi girma a kasar Habasha, ta yi zargin cewa shirin zai tarwatsa su ya kuma raba su da gonakinsu.

Jami'an tsaron kasar sun yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa masu zanga-zangar. Kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Human Right Watch' ta ce kusan mutane 400 ne aka kashe a lokacin.

A zanga-zangar wanann makon ma da al'ummun Oromo da Amhara su ka yi, an kashe kusan mutane 100.