Boko haram Ta Kashe mutane 6 A Arewacin Kasar Kamaru.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9430-boko_haram_ta_kashe_mutane_6_a_arewacin_kasar_kamaru.
Kungiyar Boko haram ta kai wani hari a arewacin kasar Kamaru wanda ya dauki  rayuwa da jikkata wasu.
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 10, 2016 14:40 UTC
  • Boko haram Ta Kashe mutane 6 A Arewacin Kasar Kamaru.

Kungiyar Boko haram ta kai wani hari a arewacin kasar Kamaru wanda ya dauki  rayuwa da jikkata wasu.

Kungiyar Boko haram ta kai wani hari a arewacin kasar Kamaru wanda ya dauki  rayukan mutane 4.

Majiyar watsa labaru ta "Africa Time"  ta nakalto majiyar tsaron kasar Kamaru na sanar da cewa; A kalla mutane 4 ne su ka kwanta dama a harin da 'yan boko haram su ka kai a jiya talata da dare a yankin da ke arewacin kasar.

Majiyar tsaron ta kamaru ta kara da cewa; Bayan hari da kungiyar ta kai a yankin na Gambarou  ta kuma cinna wuta a wata motar daukar kaya, da kuma gidaje 60.

Majiyar tsaron ta Kamaru ta kuma ce; Sojojin kasar sun kame wani dan boko haram guda bayan kashe shida daga cikinsu.

Kasar ta Kamaru dai tana daga cikin kasashen da su ke fama da matsalar boko haram wacce ta addabi kasashen da su ke makwabtaka da Najeriya.