Fira Ministan Guinea Conakry Ya Jaddada Wajabcin Zaman Lafiya Da Sulhu
Fira ministan Guinea Conakry ya jaddada yin kira ga kara samun zaman lafiya da sulhu a duk fadin kasar.
A ziyarar aikin da ya kai zuwa gunduma ta biyar da ke birnin Conakry: Fira ministan kasar Guinea Mamadi Youla ya yi kira ga al'ummar kasar kan daukan matakan kara karfafa zaman lafiya da sulhu a tsakaninsu tare da kara kaimi a fagen bunkasa ci gaban kasar.
Mamadi ya kuma jaddada cewa: Gwamnatinsa zata samar da ayyukan yi musamman ga matasa tare da kara bunkasa fagen koyar da ayyukan raya kasa da sana'o'i.
Har ila yau fira ministan kasar ta Guinea Conakry ya jaddada yin kira ga 'yan siyasar kasar da su kara bude fagen gudanar da tattaunawa da fahimtar juna a tsakaninsuda nufin ciyar da kasar gaba.