Kara Tabarbarewar Harkokin Tsaro A Kasar Sudan Ta Kudu
Rikicin kasar Sudan ta kudu zata kara tabarbarewa idan sojojin kasa da kasa suka shiga cikin kasar.
Shawarar da gwamnatin Amurka ta gabatarwa komitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ta aike da dakarun tabbatar da zaman lafiya 4000 zuwa sudan ta kudu zai kara rikita harkokin tsaro a kasar ne.
Jaridar Africa Time a shafinta na yanar gizo ta bayyana cewa idan komitin tsaro ta amince da kudurin da Amurka ta gabatar masa kan tura dakarun tabbatar da zaman lafiya daga yankin zuwa kasar Sudan ta Kudu al-amuran tsaro zasu kara rikicewa ne.
Rahoton ya kara da cewa idan kudurin bai samu karbuwa a komitin tsaron ba, ko kuma gwamnatin kasar Sudan ta kudu take amincewa da hakan, ko kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya Banki Moon ya ki amincewa da korin, kofa a bude take na adorawa kasar takunkumin sayar mata da makamai.
A halin aynzu ana ganin kasar Sudan tana cikin barazanar barkewan yaki da gaske tsakanin sojojin yan tawaye da na kwamnati a cikin yan kwanaki masu zuwa.