Zambiya : Jam'iyya Mai Mulki Ta Tafka Magudi A Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9538-zambiya_jam'iyya_mai_mulki_ta_tafka_magudi_a_zabe
Babban dan hamayya a kasar Zambiya, Hakainde Hichilema ya zargi shugaba mai barin gado, Edgar Lungu da tafka magudi a zaben shugaban kasar da yanzu haka al'ummar kasar ke ci gaba da dakon sakamakonsa.
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 12, 2016 13:34 UTC
  • Zambiya : Jam'iyya Mai Mulki Ta Tafka Magudi A Zabe

Babban dan hamayya a kasar Zambiya, Hakainde Hichilema ya zargi shugaba mai barin gado, Edgar Lungu da tafka magudi a zaben shugaban kasar da yanzu haka al'ummar kasar ke ci gaba da dakon sakamakonsa.

Mr Hichilema wanda shi ne babban dan adawa na kasar ya zargin jam'iyyar (PF) mai mulki da hada kai da hukumar zaben kasar domin jinkirta sakamakon zaben da aka kada kuri'arsa jiya Alhamis.

Jagoran jam'iyar ta (UPND) ya shaidawa manema labarai cewa, hukumar zabe na jan kafa wajen sanar da sakamakon zaben saboda 'yan daba na jam'iyya mai mulki su samu damar farmawa runfunan zabe cikin dare don canza sakamakon zaben.

Shugaba Edgar Lungu na fafatawa ne dai da Hakainde Hichilema a karo na biyu, bayan karawar da suka yi watanni 20 da suka gabata dan maye gurbin shugaba Michael Sata da ya mutu a kan karagar mulki.