Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Rwanda Da Jamhuriyar Dimukradiyar Congo
Shugabannin kasashen Rwanda da kuma Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo sun gudanar da wata tattaunawa dangane da batutuwa da suka shafi tsaro a tsakanin kasashen biyu.
Gidan radiyon Aukapi na kasar Congo ya bayar da rahoton cewa, shugaba Joseph Kabila ya gana da takwaransa na kasar Rwanda Paul kagame a jiya Juma'a a gain Gisenyi na kasar Rwanda, wanda ke kusa da iyakokin kasashen biyu.
Kabila da Kagame sun tattuna kan batun matsalolin tsaron da ake fuskanta a kan iyakin kasashen biyu, sakamakon kafa sansanoni da 'yan tawayen Hutu na kasar Rwanda suka yi a cikin Congo a kan iyaka da Rwanda, lamarin da ya kara jawo tabarbarewar harkokin tsaro a yankin.
Haka nan kuma shugabannin kasashen biyu sun tattauna batun sake kafa kwamitin da zai kara tantance iyakokin kasashen biyu.