Gobara Ta Lalata Kimanin Shaguna 200 A Kasuwar Singa Ta Kano
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i958-gobara_ta_lalata_kimanin_shaguna_200_a_kasuwar_singa_ta_kano
Rahotanni daga jihar Kano da ke arewacin Nijeriya sun bayyana cewar sama da shaguna 200 ne suka kone sakamakon wata gobara da ta tashi a yau Alhamis a kasuwar Singa da ke jihar.
(last modified 2018-08-22T06:57:50+00:00 )
Feb 18, 2016 13:38 UTC
  • Gobara Ta Lalata Kimanin Shaguna 200 A Kasuwar Singa Ta Kano

Rahotanni daga jihar Kano da ke arewacin Nijeriya sun bayyana cewar sama da shaguna 200 ne suka kone sakamakon wata gobara da ta tashi a yau Alhamis a kasuwar Singa da ke jihar.

Jaridar Vanguard ta Nijeriya ta bayyana cewar daraktan hukumar 'yan kwana-kwana ta jihar Kanon, Alhaji Balarabe Kabara ya tabbatar mata da aukuwar gobarar wanda ya ce ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiyar yau agogon Najeriya, inda ya ce wani adadi mai yawa a kasuwar sun kone, sai dai ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike don gano adadin shaguwan da gobarar ta shafa.

Sai dai jaridar ta ce wani shaidan gani da ido ya shaida mata cewa gobarar ta tashi ne a wani waje mai rukunin shaguna da suka dara 200, kuma kusan dukkaninsu gobarar ta shafe su, kamar yadda kuma gobarar ta shafi wasu wajajen ajiye kayayyakin abinci da sauran kayayyakin masarufi da suke kusa da kasuwar.

A kwanakin baya ma dai wata gobarar ta tashi a wata tsohuwar kasuwa mai tarihi a Kanon inda ta janyo hasarar gaske ga 'yan kasuwan.